A watan Yulin shekarar 2024 da ta gabata, kasar Belarus ta shiga kungiyar hadin kai ta Shanghai ko (SCO) a hukumance. Kuma a kwanan nan, shugaban kasar Aleksandr Lukashenko, ya zanta da wakiliyar babban rukunin gidajen rediyo da talibijin na kasar Sin wato CMG a takaice, a fadar gwamnatinsa, inda ya ce shigar Belarus cikin kungiyar SCO, wani kuduri ne da aka cimma bisa tsanaki, kuma an yi shi bayan zurfin tunani, duba da rawar gani da kungiyar ke kara takawa a harkokin siyasar duniya.
Lukashenko ya kara da cewa, a yau, kungiyar SCO na kara tasirinta a duniya, kuma kasarsa ma ta kasance daya daga cikin mambobin kungiyar. Ya ce, kaso 75% na adadin cinikayyar kasarsa na fitowa ne daga cinikayyar da kasarsa ke yi da kasashe mambobin kungiyar SCO, wanda hakan babban kaso ne mai girma.
Shekarar da muke ciki, “shekarar kasar Sin” ce ga kungiyar SCO. Kuma yayin da yake tsokaci game da ayyukan da kasar Sin ke aiwatarwa a matsayinta na mai rike da shugabancin kungiyar a wannan karo, Lukashenko ya bayyana cewa, kasar Sin tamkar inji ne dake inganta ci gaban kungiyar.
A cewarsa, kasar Sin tana kokarin ba da jagoranci ta hanyar aiwatar da hakikanin ayyuka, kuma tana ba da gudummawa mai tarin yawa ga kungiyar. Ya ce wannan shekara ta Sin, wadda kuma kasar ke rike da ragamar shugabancin kungiyar, tana da muhimmanci kwarai da gaske, yana kuma fatan Sin za ta kara ba da gudunmawa ta gaske ga ci gaban kungiyar SCO, da kuma kara wa kungiyar sabon kuzarin ci gaba. (Bilkisu Xin)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp