Shugaban kasar Brazil, Luiz Inacio Lula da Silva, ya bayyana cewa, zai gayyaci takwarorinsa na Rasha da China, Vladimir Putin da Xi Jinping, zuwa taron G20 na gaba, wanda zai gudana a Brazil a shekarar 2024.
Bayan kammala taron G20 da aka yi a birnin New Delhi na Indiya, firaministan kasar, Narendra Modi, ya mika ragamar shugabancin G20 ga da Silva.
- Indiya Ta Mika Wa Brazil Ragamar Shugabancin G20
- AU Ta Zama Mamba Ta Dindindin A Kasashen G20 Masu Karfin Tattalin Arziki A Duniya
Taron na gaba na taron zai gudana ne daga ranar 18-19 ga Nuwamba, 2024 a birnin Rio de Janeiro na Brazil.
“Zan gayyace su (Xi da Putin) da fatan za su zo Brazil su halarci taron,” in ji kamfanin dillancin labarai na Ani na Indiya a wani taron manema labarai.
Da Silva ya kara da cewa bai san dalilan da suka sa shugabannin Rasha da China ba su halarci taron da aka yi a New Delhi ba.
Ya kuma bayyana fatan cewa ya zuwa lokacin bude taron kolin na shekarar 2024 a Brazil, za a kawo karshen rikici a Ukraine kuma komai zai dawo daidai.
Shugaban ya bayyana batutuwan da za a tattauna yayin taron G20 a Brazil, inda ya kara da cewa wani babban nauyi ne akan kungiyarsu da ya rataya a wuyan kasar.
“Za mu sanya rashin daidaito a saman: rashin daidaiton jinsi, launin fata, ilimi, lafiya, talauci, da yunwa a gaba.
“Duniya na bukatar daidaito,” in ji Da Silva, yana mai cewa yana shirin tattaunawa kan batun sauyin makamashi, da yin kwaskwarima ga cibiyoyin kasa da kasa, da kuma yiwuwar baiwa Brazil mamba ta dindindin a kwamitin sulhu na MDD.
Taron kolin G20 mafi girma a birnin New Delhi, wanda ya gudana daga ranar Asabar zuwa Lahadin makon da ya gabata, ya tara kasashe 20 da suka hada da Bangladesh, Masar, Spain, Mauritius, Nijeriya, Netherlands, Hadaddiyar Daular Larabawa. , Oman, da Singapore.