Jiya Laraba 8 ga wannan wata, shugaban kasar Chadi Mahamat Idriss Deby ya gana da mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS kuma ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi a birnin N’Djamena, fadar mulkin kasar.
Yayin ganawar tasu, shugaba Mahamat ya taya kasar Sin murnar shirya taron kolin Beijing na dandalin tattauna hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka cikin nasara, yana mai cewa, taron kolin ya ciyar da huldar dake tsakanin sassan biyu gaba yadda ya kamata. Kuma ya nuna godiya ga kasar Sin saboda a ko da yaushe kasar tana gudanar da hadin gwiwar dake tsakaninta da kasashen Afirka bisa tushen mutunta juna, da daidaito, da kuma samun moriya tare.
- Wang Yi Zai Kai Ziyara Kasashen Namibia, Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, Chadi Da Najeriya
- Akwai Buƙatar MDD Ta Shigo Don Binciko Masu Ɗaukar Nauyin Ta’addanci A Nijeriya Daga Ƙetare
Haka kuma ya ce kasar Sin tana samar da goyon baya ga ci gaban kasashen Afirka, musamman ma kasar Chadi, baya ga nuna kwazo da himma kan kiyaye adalcin duniya. Don haka, ya ce kasarsa tana son kara karfafa cudanya da kasar Sin domin cimma muradunsu tare kuma da kiyaye moriyarsu.
A nasa bangare, Wang Yi ya yi tsokacin cewa, shugabannin kasashen Sin da Chadi sun daga huldar kasashensu zuwa huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare, lamarin da ya alamta cewa, hadin gwiwar dake tsakaninsu ya shiga wani sabon mataki. Kana har kullum kasar Sin tana nacewa kan manufar tsara al’amura daidai-wa-daida tsakanin kasa da kasa, kuma tana son kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da kasar Chadi, ta yadda za su ci gaba da nuna wa juna goyon baya kamar yadda suke yi a halin yanzu.
Hakazalika, ya ce kasar Sin tana fatan za ta yi kokari tare da Chadi domin aiwatar da muhimman muradun da shugabannin kasashen biyu suka cimma, tare kuma da samar da tallafi ga ci gaban kasar Chadi, da gina kyakkyawar makomar bai daya ta Sin da Afirka a sabon zamani.
Duk dai a wannan ranar, Wang Yi ya gana da firayin ministan kasar Chadi Allah-Maye Halina, kana ya yi shawarwari da takwaransa na kasar Abderaman Koulamallah a birnin N’Djamena. (Mai fassara: Jamila)