Shugaban rukunin gidajen rediyo da talibijin na kasar Sin ko CMG Shen Haixiong, ya gana da jagoran hukumar yaki da shan kwayoyin kara kuzari ga ‘yan wasan motsa jiki ko WADA mista Witold Banka, wanda ke halartar gasar wasanni ta Asiya a birnin Hangzhou.
Yayin zantawar ta su, shugabannin 2 sun yi musayar ra’ayi game da batutuwan da suka shafi gasar ta Hangzhou, da gasar Olympics ta Paris, da kuma batun ilmantar da jama’a game da yaki da shan kwayoyin kara kuzari. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp