Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya ce bisa gayyatar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi masa, shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, zai ziyarci kasar Sin tsakanin ranakun Laraba 3 zuwa Juma’a 5 ga watan nan na Disamba.
Lin Jian, ya bayyana hakan ne a yau Litinin, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, yana mai cewa wannan ne karo na hudu da shugaba Macron zai kawo ziyara kasar Sin. Kuma ziyarar tasa za ta zamo ramako ga ziyarar aiki da shugaba Xi ya gudanar a Faransa cikin shekarar da ta gabata, albarkacin bikin cika shekaru 60 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Faransa.
A cewar Lin, yayin ziyarar ta wannan karo, shugabannin kasashen biyu za su zanta dangane da matakan bunkasa alakar Sin da Faransa a sabin yanayin da ake ciki, kuma za su zurfafa musaya kan muhimman batutuwan kasa da kasa da na shiyyoyi masu jan hankali. (Saminu Alhassan)














