Shugaban Hukumar Zaɓe ta Jihar Bauchi (BASIEC), Alhaji Ahmad Makama Hardawa, ya rasu a ranar Talata, 29 ga watan Yuli, 2025 a Abuja bayan fama da gajeriyar rashin lafiya.
Makama, wanda ya taɓa zama Kwamishinan Hukumar Zaɓe (INEC) a jihohin Taraba da Nasarawa, ya rasu bayan shafe shekaru yana yi wa ƙasa hidima.
- Gwamnan Kaduna Ya Sauke Kwamishinan Yaɗa Labarai, Ya Maye Gurbinsa Da Maiyaki
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga 45 A Jihar Neja
Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Muhammad, ne ya bayyana mutuwar, inda ya yi alhini da juyayi wannan babban rashi.
A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Mukhtar Gidado, ya fitar, gwamnan ya bayyana Makama a matsayin mutum mai gaskiya, riƙon amana, da kishin ƙasa.
Gwamna Bala ya ce Makama ya taka rawar gani a matsayin shugaban BASIEC, inda ya jagoranci zaɓuka cikin gaskiya da adalci, ya kuma taimaka wajen gina dimokuraɗiyya.
Ya ce biyayyarsa ga doka da oda ya sa ya samu girmamawa daga abokan aikinsa da jama’a gaba ɗaya.
Gwamnan ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalansa, ’yan uwansa, abokansa da ma al’ummar masarautar Hardawa da ta Misau.
Ya roƙi Allah Ya gafarta masa, Ya jikansa, ya kuma sanya shi a Aljanna.
LEADERSHIP Hausa ta gano cewa aikin ƙarshe da Makama ya jagoranta a matsayin shugaban BASIEC shi ne zaɓen cike gurbi na shugaban ƙaramar hukumar Shira da mataimakinsa, a ranar 24 ga watan Mayu, 2025.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp