Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya yi kira da a sake fasalin tsarin zabe gabanin zabe masu zuwa na 2027.
Farfesa Yakubu ya yi wannan kira ne yayin jawabinsa na bude taron kwanaki biyu tsakanin hukumarsa da mambobin kwamitin hadin gwiwa na majalisar dokoki kan harkokin zabe a Legas. Taron ya tattaro mambobin hukumar, ‘yan majalisar tarayya, masu ruwa da tsaki a zabe, da abokan huldar don magance kalubalen da ke tasowa a bangaren zabe.
- INEC Ta Musanta Korar Farfesa Yakubu A Matsayin Shugaban Hukumar
- Shimfida A Kan Aikin Hajji Da Bayani A Kan Mikatin Da Manzon Allah (SAW) Ya Sa
Yakubu ya yi maraba da mahalarta taron, yana mai cewa taron ya ba da dama ta musamman don inganta tsarin zaben Nijeriya ta hanyar sake duba dokoki da musayar kwarewa. Ya tuna da irin wannan koma baya a watan Maris na 2020, wanda ya haifar da soke aiwatar da sabuwar dokar zabe ta 2022.
A cwarsa, wannan ne karo na farko da ‘yan majalisa, INEC, da masu ruwa da tsaki suka tattauna muhimman al’amurran da suka shafi dokokin zabe, gami da kirkire-kirkire na fasaha, bin shari’a, da shawarwarin masu sa ido.
Shugaban INEC ya jaddada muhimman ci gaban da ya samo asali daga sauye-sauyen da suka gabata da suka hada da fadada jaddawalin zabe, gyare-gyare don ba da damar kwanaki 180 tsakanin zaben fid da gwani na jam’iyya da zabe daga kwanaki 60 ya warware jinkirin kayan aiki. Ya ce wannan ya tabbatar da cewa an gudanar da babban zaben 2023 ba tare da jinkirta ba, a karon farko tun 2010.
Ya ce wani ci gaba kuma ya hada da samar da kayan aiki na cikin gida, yana mai cewa a karon farko tun 1999, an buga dukkan kayan zabe masu muhimmanci a Nijeriya,
Farfesa Yakubu ya bayyana kalubalen da ke bukatar kulawar majalisa, da suka hada da karfafa goyon bayan doka ga sabbin abubuwa na INEC, kamar tsarin zabe da na’ura, rage shari’a bayyana rikice-rikice a cikin dokokin zabe da amincewa da shawarwarin da aka bayar a baya na gyare-gyare kwamitocin ciki har da Uwais (2009), Lemu (2011), da kuma Nnamani (2017).
Shugaban INEC ya jaddada cewa irin wannan lamari yana ba da gudummawa mai yawa fiye da sauraren kwamitocin da aka saba, wanda ke ba ‘yan majalisa damar samun fahimtar farko game da kalubalen gudanar da zabe. Ya kuma yaba da goyon bayan abokan hulda suke bayarwa wajen habaka zaben Nijeriya.
Yayin da ake ci gaba da lalubo hanyar dinke bakin zaren, INEC na shirin musayar basira tare da ‘yan majalisa don jagorantar wasu gyare-gyare ga kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999, wanda aka yi wa kwaskwarima da dokar zabe.
A cewar FarfesaYakuba, manufar ita ce karfafa tsarin zaben Nijeriya gabanin zabe na gaba a 2027.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp