Shugaban kasar Jamhuriyar Congo Denis Sassou-Nguesso ya bayyana a hirarsa da wakilin babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG a kwanakin baya cewa, jawabin shugaban kasar Sin Xi Jinping a gun taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC yana da babbar ma’ana, inda ya gabatar da ayyukan hadin gwiwa 10 na zamanintar da Sin da Afirka tare, wadanda suka kasance manufofi da matakai da bangarorin biyu za su yi kokari tare a shekaru 3 masu zuwa.
Shugaba Sassou ya kara da cewa, jawabin shugaba Xi ya tabo dukkan fannoni wajen raya dangantakar dake tsakanin Afirka da Sin, kamar su tattalin arziki, da hada-hadar kudi, da batutuwan zamantakewar al’umma, da mu’amalar al’adu, da sada zumunta, da kuma kirkire-kirkire da fasahohin zamani.
Kuma idan aka dauki matakan da suka dace, ba shakka za a cimma buri a dukkan fannonin da bude sabon babi na raya dangantakar dake tsakanin Afirka da Sin. Wannan ya shaidawa duniya hanyar zaman tare a tsakanin kasa da kasa, da jama’arsu bisa tushen nuna goyon baya ga juna da samun wadata tare. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp