Shugaban jamhuriyar Congo Denis Sassou Nguesso, ya halarci bikin kaddamar da aikin gina tituna da kamfanin gina hanyoyin mota da gadoji na kasar Sin (CRBC) ya kaddamar a lardin Sangha na arewacin kasar.
A yayin bikin da ya gudana ranar Asabar, ministan raya kasa, kayayyakin aikin yankuna da kuma manyan ayyuka, Jean-Jacques Bouy, ya bayyana muhimmancin aikin ga ci gaban tattalin arziki da zamantakewar kananan hukumomi, yana mai bayyana yadda kamfanin CRBC ke kokarin gudanar da ayyuka masu inganci a cikin shekaru a kasar. Bayan bikin ne kuma, shugaban na Congo ya aza harsashin tubalin aikin.
Titin mai tsawon kilomita 47, zai hada birnin Ouesso da garin Pokola. Aikin ya kuma hada da gina wata gada mai tsawon mita 616 a kan kogin Sangha. (Ibrahim)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp