Shugaban jam’iyyar APC mai mulki a jihar Neja, Haliru Zakari Jikantoro, ya yi murabus daga mukaminsa ba tare da bayyana wasu dalilai ba.
Jikantoro ya sanar da murabus din nasa ne bayan taron kwamitin ayyuka na jam’iyyar a sakatariyar jam’iyyar APC na Jiha da ke Minna, a gaban babban mai baiwa gwamnan jihar shawara kan harkokin siyasa, Alhaji Mohammed Nma Kolo.
Jikantoro ya ce, “Ni amfani da wannan dama ina sanar da yin murabus daga mukamina na shugaban jam’iyyar APC bisa radin kaina.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp