Shugaban jam’iyyar APC na shiyyar Ibadan da ke jihar Oyo, Alhaji Bashiru Ajibade, ya jagoranci wasu daruruwan mambobin jam’iyyaar APC wajen sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP.
Taron sauka shekar wanda ya gudana a makarantar IMG da ke garin Eleta, daga cikin fitattun ‘yan APC da suka fice daga jam’iyyar sun hada da Alhaji Abass Najeemdeen Gbayawu, Alhaji Bolaji Akinyemi Kosigiri, Engr Kayode Arowolo, da Barrister Rotimi Okeowo, gami da wasu.
Da ya ke magana a madadin jagororin wanda suka sauya shekar, Prince Olumuyiwa Akinbiyi ya lura kan cewa basu gamsu da yadda aka yi muna-muna wajen zaben fitar da gwani na jam’iyyar APC ba, wanda suka zargi wasu shafaffu da mai na jam’iyyar da yin dauki daura a jihar.
A cewarsa, sun fita daga jam’iyyar ne tare da mafiya yawa daga cikin magoya bayansu domin mara baya ga shirin gwamna Saye Makinde na zarcewa a karo na biyu.
Masu sauya shekar da suka samu tarba a madadin gwamna Makinde daga Chief Bayo Lawal, darakta janar na gangamin yakin kamfen din gwamna Seyi Makinde, da shugaban jam’yyar APC a shiyyar Ibadan ta kudu maso gasas, Emmanuel Alawode dA Kazeem Adeniyi Bibire, hadimin gwamna kan harkokin kananan hukumomi da lamuran masarautu.