Allah ya yi wa mataimakin shugaban kamfanin jirgin sama na Max Air, Alhaji Bashir Bara’u Mangal rasuwa.
Marigayin dan uwa ne ga fitaccen dan kasuwar nan dan asalin Jihar Katsina, Alhaji Dahiru Mangal.
- Hadin Gwiwar Afirka Da Sin Hadin Gwiwa Ce Ta Sada Zumunta A Tsakanin ’Yan Uwa
- Baje Kolin Zuba Jari Ya Nuna Amincewar Duniya Game Da Farfadowar Tattalin Arzikin Kasar Sin
Marigayin ya rasuwa a wani asibiti da ba a bayyana sunansa ba a babban birnin Tarayya, Abuja.
Ya rasu ne bayan ya yi jinya ta tsawon lokaci, insa ya sha fama da rashin lafiya.
Tuni aka yi jana’izarsa da misalin 6 na yammacin yau a Katsina.
Tuni manyan mutane daga cikin gida da wajen kasar nan suka shiga mika sakon ta’aziyyarsu ga iyalan mamacin.