Tsohon gwamnan Jihar Kano, Ibrahim Shekarau, ya ce bai kamata ‘yan Nijeriya su damu da batun tsarin karba-karba, sai dai su ba da fifiko kan dan takarar shugaban kasa na 2027 maki nagarta.
An dade ana tafka muhawara kan yadda mulki zai koma yankin arewacin kasar a shekarar 2027.
- Da Rancen Naira Tiriliyan 13 Za A Cike Gibin Kasafin Kudin 2025 — Edun
- Xi Ya Halarci Bikin Dawowar Yankin Musamman Na Macao Kasar Sin Da Rantsar Da Sabuwar Gwamnati
Sai dai kuma akwai hujjar cewa yankin kudancin kasar nan da ya samar da Shugaban kasa Bola Tinubu, har yanzu bai cika shekaru takwas a kan karagar mulki ba.
Shekarau yana da ra’ayin cewa a halin yanzu bai kamata yankin ya maida hankali ba wajen dole sai shugaban kasa ya fita daga wannan bangare, sai dai a mayar da hankali wajen samun nagartaccen shugaban kasa.
“Ya kamata dukkan jam’iyyu su fito da tsare-tsarensu wanda zai bayar da damar fito da nagartattun ‘yan takara a 2027.
“Amma ‘yan Nijeriya kadai a yanzu za su iya yanke shawara, damuwarmu ita ce mu duba ‘yan takarar da jam’iyyun suka fitar.
“Kalubalenmu shi ne, dukkan jam’iyyu su bai wa ‘yan Nijeriya nagartattun ‘yan takara da za a samu mafi kyawun zabi a lokacin zaben 2027.
“Amma idan ka ba mu dukkan munanan ‘yan takara, ba za mu zabi mafi alheri ba,” in ji Shekarau a gidan talabijin na Channels.