Tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Sanata Abdulaziz Yari, Mai wakiltar Zamfara ta yamma a Majalisar Dattawa, ya bayyana cewa, Shugaban Kasa ne ke iya magance matsalar tsaro ba Gwamnoni ba.
Sanata Yari ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke amsar rahotonnin Kwamitin tallafin Abincin Azumi da Sallah a karamar hukumar Mafara da ke jihar Zamfara.
- Yanzu-yanzu: Hatsaniya Ta Kaure Tsakanin Sojoji Da Matasa A Gashuwa
- ‘Yansanda Sun Kama Tirelar Sata Da Kayan Miliyan 30 A Bauchi
Yari ya bayyana cewa, gwamnoni na iya kokarinsu na ganin sun yi abinda ya kamata dan kare al’umma daga matsar hare-haren ‘yan bindiga, amma abun ya ci tura saboda basu ke da ruwa da tsaki ba wajan tafiyar da Jami’an tsaro sai Shugaban Kasa.
“Da Shugaban Kasa zai ba wa gwamnoni damar ganinsa kai tsaye duk lokacin da matsalar tsaro ta taso, da an dakile matsalar ‘yan Ta’addan a duk inda suke a fadin Kasar nan.” In ji Yari.