Kwanan nan, wakiliyar CMG ta zanta da shugaban kasar Azerbaijan Ilham Aliyev wanda ya kawo ziyarar aiki a kasar Sin. A yayin zantawar, shugaba Aliyev ya waiwayi dadadden tarihin cudanyar kasashen biyu da ma zumuncin da ke tsakaninsu, kuma ya yi imanin da cewa, kasancewar dukkansu kasashe masu tasowa ne, kasashen biyu za su hada hannu wajen bayar da karin gudummawa wajen kiyaye zaman lafiya da ci gaba a duniya.
Shugaba Aliyev ya ce, “Muna ganin kasar Sin jagora ce ga kasashe masu tasowa na duniya, kuma tana taka rawar gani a wajen hada kan kasa da kasa, musamman ma wajen yayata ruhin Bangdun, ciki har da martaba ikon mulki da cikakkun yankunan kasa na sauran kasashe, da rashin tsoma baki cikin harkokin gidan kasashe, da kiyaye zaman daidaito da cudanyar bangarori daban daban, da nuna kin yarda da babakere da sauran danniya a duniya daga kowace kasa ko kungiya.”(Lubabatu)