Shugaban kasar Sin Xi Jinping da uwargidansa Peng Liyuan, sun aike da sakon taya murna a yau Asabar, ga Sarki Charles na III da Sarauniya Camilla kan tabbatar da nadinsu a hukumance.
A sakon nasu, Xi da Peng sun ce duniya na fuskantar manyan sauye-sauye masu sarkakiya, kuma kasa da kasa na fuskantar kalubalen da ba a taba ganin irinsu ba.
Sun kara da cewa, a matsayinsu na mambobin dindindin a Kwamitin Sulhu na MDD, ya kamata Sin da Birtaniya, su hada hannu wajen inganta yanayin da ake ciki na rungumar zaman lafiya da ci gaba da cin moriyar juna.
A cewarsu, a shirye Sin take ta hada hannu da Birtaniya wajen inganta abota tsakanin al’ummunsu, da fadada hadin gwiwar moriyar juna da zurfafa mu’amala da musayar al’adu tsakanin jama’arsu ta yadda kasashen biyu da duniya baki daya, za su amfana da dangantaka mai karko da alfanu.
A yau Asabar aka tabbatar da nadin Sarki Charles na III a matsayin Sarkin Ingila a hukumance, yayin wani kasaitaccen biki da ba a ga irinsa ba cikin shekaru 70.(Fa’iza Mustapha)