• English
  • Business News
Monday, October 27, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Isa Birnin Riyadh Kasar Saudiyya

by CMG Hausa
3 years ago
Xi Jinping

LABARAI MASU NASABA

Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

Da yammacin ranar 7 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya isa birnin Riyadh na kasar Saudiyya. Bisa shirin da aka tsara, daga yau Laraba 7 zuwa 10 ga watan nan na Disamba, bisa gayyatar Sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud na Saudiyya, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarci taron koli na farko na Sin da kasashen Larabawa, da taron koli na Sin da kasashen kungiyar hadin kan yankin Gulf ko (GCC), wanda zai gudana a birnin Riyadh na kasar Saudiyya. Kaza lika shugaban na Sin zai gudanar da ziyarar aiki a masarautar ta Saudiyya.

Game da hakan, a yayin taron manema labarai na yau Laraba, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Sin Mao Ning, ta gabatar da bayanai, inda ta ce taron kolin na farko na kasar Sin da kasashen Larabawa, wanda shugaba Xi Jinping zai halarta, shi ne aiki mafi girma cikin harkokin diflomasiyya tsakanin Sin da kasashen Larabawa, tun bayan kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin, zai kuma kasance wani muhimmin ginshiki a tarihin alakar Sin da kasashen Larabawa.

Mao ta kara da cewa, kasashen kungiyar hadin kan yankin Gulf ko GCC, su ne muhimman abokan hadin gwiwar Sin a gabas ta tsakiya. Kuma cikin sama da shekaru 41 da suka gabata, alakar Sin da GCC na ta kara habaka daga dukkanin fannoni, cikin sauri da zurfafar ayyuka, inda alakar sassan biyu ke ta haifar da alheri na hadin gwiwa, a fannonin raya tattalin arziki da cinikayya, da makamashi, da hada-hadar kudade, da zuba jari. Sauran sassan sun hada da na manyan fasahohi, da harkokin samaniya, da raya yaruka da al’adu, wanda hakan ya sanya Sin din zama a sahun gaba, a fannin hadin gwiwa da kasashen gabas ta tsakiya. (Saminu Alhassan)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai
Daga Birnin Sin

Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

October 26, 2025
Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya
Daga Birnin Sin

Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

October 26, 2025
Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%
Daga Birnin Sin

Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%

October 26, 2025
Next Post
“Dalilanmu Na Cafke Fitaccen Mawaki D’banj” —ICPC

“Dalilanmu Na Cafke Fitaccen Mawaki D'banj” —ICPC

LABARAI MASU NASABA

Xi Jinping

Tsohon Gwamnan Jigawa, Lamido Ya Bayyana Aniyar Takarar Shugabancin Jam’iyyar PDP Na Ƙasa

October 27, 2025
Sojoji Sun Kashe ‘Yan ta’adda 10, Sun Ƙwato Makamai A Borno

Sojoji Sun Kashe ‘Yan ta’adda 10, Sun Ƙwato Makamai A Borno

October 27, 2025
Hatsarin Jiragen Ruwa

Matasa 5 Sun Mutu A Hatsarin Jirgin Ruwa A Gombe

October 27, 2025
Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

October 26, 2025
Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

October 26, 2025
Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

October 26, 2025
“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

October 26, 2025
Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%

Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%

October 26, 2025
Dalilin Da Suka Sa Hisbah Ta Dakatar Da Auren Ƴan TikTok A Kano

Dalilin Da Suka Sa Hisbah Ta Dakatar Da Auren Ƴan TikTok A Kano

October 26, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Ma’aikacin Gwamnati Na Shekarar 2025, Dakta Zacch Adedeji

October 26, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.