A yammacin yau Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tattauna da takwaransa na kasar Brazil Luiz Inacio Lula da Silva, wanda ke ziyarar aiki a kasar Sin a babban dakin taron jama’a dake nan birnin Beijing.
A yayin tattaunawar, Xi Jinping ya nuna cewa, bisa ga yanayin da duniya ke ciki na fuskantar sauye-sauye da rikice-rikice, kamata ya yi kasashen Sin da Brazil su kiyaye ainihin manufar daukar nauyin ci gaban bil’adama, da sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na ci gaban duniya, don kara sa kaimi ga gina al’umma mai kyakkyawar makomar bai daya ta kasashen biyu, da zurfafa hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare, da kuma yi aiki tare don jagorantar kasashe masu tasowa na duniya su karfafa hadin kansu.
- Gwamna Zamfara Ya Raba Katin ATM Ga Mutane 400,000 Da Suka Ci Gajiyar Shirin ‘Cash Transfer’ A Jihar
- An Nuna Fasahar Waken Pingtan Na Kasar Sin A Najeriya
Lula ya ce Brazil da Sin suna mutunta juna kuma makomarsu iri daya ce.
Ya kuma bayyana cewa, dangantakar da ke tsakanin kasarsa da kasar Sin aba ce da wasu daga waje ba za su taba iya kassarawa ba, kuma ba za su iya kafa mata kahon zuka ko ruguza ta ba. Inda ya kara da cewa, Brazil tana son zurfafa hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare da kasar Sin, da kara matse kaimi ga gina al’ummar kasar Sin da Brazil mai makoma guda, da gina duniya mai cike da adalci, da zaman lafiya da wadata, da kuma zama ababen koyi ga dukkan kasashe.
Bayan tattaunawarsa da shugaba Xi, shugabannin kasashen biyu, sun shaida rattaba hannu kan yarjeniyoyin hadin gwiwa guda 20 a fannonin dabarun ci gaba, da kimiyya da fasaha, da aikin gona, da tattalin arziki na fasahohin zamani, da sha’anin kudi, da kuma kafofin watsa labarai.
Kazalika, shugabannin kasashen biyu sun kuma gana da manema labarai a tare.
Bangarorin biyu dai sun fitar da sanarwar hadin gwiwa kan karfafa gina al’ummar Sin da Brazil mai makoma guda domin kara tabbatar da samuwar duniya mai cike da adalci, wacce za ta kasance mai dorewa cikin nagarta, da kara hada karfi da karfe wajen karfafa damawa da sassa daban-daban a sha’anin duniya, tare da ba da sanarwar hadin gwiwa game da rikicin Ukraine.
Kafin ganawar dai, shugaba Xi Jinping da uwargidansa Peng Liyuan, sun shirya bikin maraba ga Lula da uwargidansa a dandalin da ke wajen kofar gabas na babban zauren taron al’umma. (Bilkisu Xin/Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp