ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Zai Yi Jawabi A Yayin Bude Taro Zagaye Na 2 Na Yarjejeniyar COP15

by CMG Hausa
3 years ago
COP15

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta sanar da cewa, a gobe Alhamis, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai gabatar da jawabi ta kafar bidiyo, yayin bude taro zagaye na biyu, na wakilan bangarorin da suka sanya hannu kan jarjejeniya kasancewar mabambantan halittu karo na 15 ko COP15.

Sannan, Shugaban taron MDD kan wanzuwar mabanbantan halittu, kuma ministan ma’aikatar kula da muhalli da muhallin halittu ta kasar Sin Huang Runqiu, ya yi kira ga sassa masu ruwa da tsaki da su tashi tsaye, wajen jajircewa, da nuna hikima da kwazo, domin toshe gibin dake akwai, da sabani, ta yadda za a cimma nasarorin da aka sanya gaba.

  • An Shirya Gudanar Da Kashi Na Biyu Na Taron COP15

Huang Runqiu ya yi tsokacin ne a jiya Talata, yayin taron manema labarai, karkashin taron sassan da suka amince da yarjejeniyar MDD game da wanzuwar mabanbantan halittu karo na 15 ko COP15 a takaice.

ADVERTISEMENT

Huang ya kara da cewa, sakamakon rawar da daukacin sassan masu ruwa da tsaki a yarjejeniyar suka taka, taron ya cimma manyan nasarori.

Cikin su har da amincewa da shawarwari guda 23, wadanda suka kai kaso daya bisa uku na jimillar shawarwarin da ake bukata wajen cimma nasarar taron. Ya ce a wasu sassa masu muhimmanci ma, dukkanin bangarorin sun yin musayar ra’ayi mai zurfi kan matsayar su da mahangar su.

LABARAI MASU NASABA

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

An bude taron game da yarjejeniyar MDD mai nasaba da wanzuwar halittu mabanbanta ne a makon jiya, kuma taron ya shiga lokaci mafi muhimmanci, yayin da ya rage mako guda a fitar da kundin da zai yi bitar matakan sauya asara, da koma-bayan da aka samu, game da wanzuwar mabanbantan halittu.

Bisa tanadin taron, za a gudanar da zaman dandalin ministoci tsakanin ranakun 15 zuwa 17 ga watan Disambar nan, domin warware batutuwa masu sarkakiya dake cikin kundin.
Da take tsokaci yayin taron manema labaran da ya gudana, babbar sakatariyar taron Elizabeth Maruma Mrema, ta ce “Muna bukatar wannan tattaunawa, domin cimma nasarar fitar da kyakkyawan tsari mai inganci, na gudanar da ayyukan da za su dakatar da asarar da ake tafkawa, a fannin wanzuwar halittu mabanbanta, tare da share fagen farfado da fannin yadda ya kamata”. (Safiyah Ma, Saminu Alhassan)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara
Daga Birnin Sin

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka
Daga Birnin Sin

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin
Daga Birnin Sin

Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

December 20, 2025
Next Post
Qatar 2022: Faransa Ta Doke Morocco A Wasan Zagayen Kusa Da Na Karshe

Qatar 2022: Faransa Ta Doke Morocco A Wasan Zagayen Kusa Da Na Karshe

LABARAI MASU NASABA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

December 21, 2025
Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

December 21, 2025
Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

December 21, 2025
Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.