Da misalin karfe 3 na safe jiya Talata ne wani jirgin ruwan kamun kifi na kasar Sin ya kife a yankin tsakiyar tekun Indiya, inda ma’aikatan jirgin 39 suka bace, ciki had da ’yan kasar Sin 17, da ’yan kasar Indonesiya 17, da ’yan Philippines 5. Ya zuwa yanzu ba a gano su ba tukuna, sai dai kuma ana ci gaba da neman su.
Bayan kifewar jirgin, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bukaci ma’aikatar kula da aikin gona da yankunan karkara ta kasar, da ma’aikatar kula da sufuri da zirga-zirga ta kasar, da kuma mahukuntan lardin Shandong, da su aiwatar da tsarin ko-ta-kwana, su tantance lamarin, kana su kara tura masu aikin ceto, tare da kula da ayyukan ceto tsakanin kasa da kasa a kan teku, su kuma yi iyakacin kokarin ceton wadanda suka bace.
Haka kuma, shugaban Sin ya ce wajibi ne ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, da ofisoshin jakadancin kasar Sin a kasashe masu ruwa da tsaki kan batun, su inganta tuntubar mahukuntan wurin, domin gudanar da ayyukan ceto yadda ya kamata.
Har ila yau, shugaba Xi ya bukaci a kauracewa aukuwar hadari a lokacin gudanar da aiki a teku mai nisa, da ba da gargadi kan barazana, a kokarin tabbatar da tsaron lafiyar jama’a da kuma dukiyoyinsu. (Tasallah Yuan)