Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira ga lardin Jiangsu dake gabashin kasar Sin da ya wuce gaba, wajen aiwatar da manufofin bunkasa zamanantar da kasar Sin.
Xi Jinping ya yi wannan kira ne yayin da yake rangadi a lardin na Jiangsu, tun daga ranar Laraba zuwa Juma’ar nan.
Kaza lika, shugaba Xi ya bukaci lardin da ya ci gaba da zama abun koyi wajen ingiza sauye-sauye, da kirkire-kirkire, da samar da ci gaba mai inganci, tare da ba da karin gudummawa ga kokarin Sin, na kafa sabon ginshikin samar da ci gaba.
Shugaban na Sin ya kuma jinjinawa kwazon lardin Jiangsu, a fannin kafa tushen masana’antu, da samar da albarkatun raya ilimi da kimiyya, da kyautata yanayin kasuwanci, da fadada kasuwanni.
Yayin rangadin da shugaban na Sin ya kammala, ya ziyarci biranen Suzhou da Nanjing, ya kuma ganewa idanunsa wurare da dama, ciki har da yankin masana’antu, da kamfanoni, da wuraren tarihi da na raya al’adu, da wani dakin gwaje-gwajen kimiyya.
Bugu da kari, da yammacin jiya ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ziyarci dakin gwaje-gwaje na Zijinshan, da rukunin kamfanin NARI dake birnin Nanjing, babban birnin lardin Jiangsu, domin kara fahimtar yadda ake inganta manyan ayyukan kimiyya da fasaha, da raya kamfanonin kere-kere na zamani, da kuma kokarin samun ci gaba mai inganci da sauransu.
An kafa dakin gwaje-gwaje na Zijinshan ne a shekarar 2018, yanzu haka, akwai masana kimiyya da fasaha sama da dubu 1 dake aiki a dakin gwajin, wadanda suka cimma muhimman sakamako kan ayyukan sadarwar B5G/6G.
Kamfanin Nari, babban kamfani ne a fannonin makamashi, wutar lantarki da sarrafa masana’antu a kasar Sin, kayayyaki da ayyukan da kamfanin ke samarwa, sun shafi kasashe da yankuna fiye da 100 na duniya. Haka kuma kamfanin ya taba lashe lambobin yabo guda 86 da kasar ta samar a fannin ci gaba na kimiyya da fasaha. (Masu Fassarawa: Maryam Yang, Saminu Alhassan)