Babban Sakataren kwamitin kolin JKS, kana shuaban kasar Sin Xi jinping ya ziyarci kauyukan da ambaliyar ruwa ta shafa a yankunan karkarar birnin Shangzhi na lardin Heilongjiang dake arewa maso gabashin kasar Sin a yau Alhamis.
A kauyen Longwangmiao, Xi ya shiga cikin gonaki domin duba irin tasirin da ambaliyar ruwa ta yi wa gonakin shinkafa. Ya kuma duba yadda ake aikin gyara gidaje da ababen more rayuwa da suka lalace a yayin da yake tattaki kan tituna.
Da yake ziyartar gidajen mutanen kauyukan domin sanin asarar da suka yi da kuma wadatar kayayyakin yau da kullum. Xi ya karfafa musu gwiwa don shawo kan matsaloli. Ya bayyana fatan nan ba da dadewa ba za su ci gaba da tafiyar da rayuwarsu yadda ya kamata, kuma rayuwarsu za ta ci gaba da inganta. (Mohammed Baba Yahaya)