A yau Asabar, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da firaministan kasar Masar Mostafa Madbouly, a birnin tashar ruwa na Tianjin dake arewacin kasar Sin.
Yayin zantawarsu, shugaba Xi ya ce alakar Sin da Masar na cikin wani yanayi mafi kyau a tarihi, ya kuma yi kira da a yi amfani da damar bikin cika shekaru 70 da kafuwar huldar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu a shekara mai zuwa, wajen cimma nasarar gina al’ummar Sin da Masar mai makomar bai daya a sabon zamani, da kara bayar da gudummawa don wanzar da zaman lafiya da daidaito a duniya, da bunkasa ci gaba da walwalar sassan kasa da kasa.
A dai yau din, shugaba Xi ya gana da firaministan Cambodia Hun Manet, da mukaddashin shugaban Myanmar, Min Aung Hlaing, da firaministan Nepal KP Sharma Oli, da shugaban kasar Kazakhstan Kassym-Jomart Tokayev, wadanda suka isa birnin Tianjin domin halartar taron koli na kungiyar hadin kai ta Shanghai wato SCO na bana.
A gobe Lahadi ne za a bude taron kolin na kungiyar SCO na shekarar bana, wanda zai gudana a birnin na Tianjin, har zuwa jibi Litinin 1 ga watan Satumba. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp