Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da firaministan Spaniya Pedro Sanchez, da na Malaysia Datuk Seri Anwar Ibrahim da na Singapore Lee Hsien Loong, a yau Juma’a a birnin Beijing.
Yayin ganawarsa da firaministan Spaniya, shugaba Xi ya ce, Sin na nacewa ga yayata salonta na zamanantar da kanta ta kowacce fuska ta hanyar ci gaba mai inganci, wanda zai kara samar da kasuwa mai fadi da karin damarmakin hadin gwiwa ga Spaniya da sauran kasashen duniya. Ya ce Sin ta shirya hada hannu da Spaniya, wajen daukar cikar dangantakarsu shekaru 50 da kulluwa a matsayin wani sabon mafari na zurfafawa da karfafa hadin gwiwar moriyar juna a tsakaninsu.
Da yake ganawa da firaministan Malaysia, shugaban ya ce a bana ake cika shekaru 10 da kulla huldar abokantaka da hadin gwiwa daga dukkan fannoni bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Malaysia, kana a badi za a cika shekaru 50 da kasashen biyu suka kulla huldar diflomasiyya a tsakaninsu. Kuma yayin ziyarar firaministan na Malaysia a wannan karo, kasashen biyu sun cimma matsaya kan gina al’umma mai makoma ta bai daya ta Sin da Malaysia, wadda tabbas za ta bude sabon babi a tarihin dangantakarsu.
A ganawa da firaministan Singapore kuwa, shugaba Xi ya bayyana cewa, kasar Sin ta na daukar dangantakarta da Singapore da muhimmanci a tsarin diflomasiyya ta makwabtaka. Ya ce a shirye Sin take ta karfafa tuntubar juna da Singapore da zurfafa hadin gwiwarsu da tabbatar da nagarta a matsayin alama ta dangantakar kasashen biyu. (Fa’iza Mustapha)