Da yammacin yau Jumma’a 28 ga wata ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da takwarorinsa na kasashen Mauritaniya da Burundi, wato Mohamed Ould Cheikh Ghazouani, da Evariste Ndayishimiye, wadanda suka iso birnin Chengdu na kasar Sin, don halartar bikin kaddamar da gasar wasannin motsa jiki ta daliban jami’o’in kasa da kasa a lokacin zafi karo na 31, tare da ziyartar kasar.
A ganawarsa da shugaban Mauritaniya, shugaba Xi ya ce, tun da suka kulla dangantakar diflomasiyya shekaru 58 da suka gabata har zuwa yanzu, Sin da Mauritaniya suna girmama juna, da mara wa juna baya, tare da kulla dadadden zumunci. Kuma Sin ta gode wa Mauritaniya, saboda goyon-bayan da take ba ta kan wasu muhimman batutuwan dake shafar babbar moriyarta. Ya ce ya dace kasashen biyu su ci gaba da nuna wa juna goyon-baya, da samar da ci gaba tare, a wani kokari na kiyaye muradunsu, da shimfida adalci a duk fadin duniya.
Har wa yau, a ganawarsa da shugaban Burundi, shugaba Xi ya ce, kasashen biyu abokan juna ne na ko da yaushe, wadanda har kullum suke girmama juna, da samar da ci gaba kafada da kafada. A halin yanzu, kasashen biyu suna cikin muhimmin lokaci na raya kasa, inda kasar Sin take son kara bunkasa mu’amalar manyan tsare-tsare na samar da ci gaba tare da Burundi, da zurfafa hadin-gwiwa, don kara samun moriya da ci gaba tare. (Murtala Zhang)