A yau Asabar din nan ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon ta’aziyya ga Sarkin Morocco Mohammed VI akan wata girgizar kasa mai karfi da ta afku a kasar ta Morocco da ta yi sanadin asarar rayuka da dukiyoyi.
Xi ya jajantawa wadanda abin ya shafa, ya kuma jajantawa iyalan wadanda suka rasu da wadanda suka jikkata a madadin gwamnati da jama’ar kasar Sin.
Ya bayyana imaninsa cewa, a karkashin jagorancin Sarki Mohammed VI, gwamnatin kasar Morocco da al’ummarta zasu shawo kan wannan bala’in da kuma sake gina muhallansu a kan lokaci. (Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp