Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya mika sakon gaisuwa da fatan alheri ga dukkan ma’aikata a kasar, gabanin ranar ma’aikata ta duniya dake gudana a ranar 1 ga watan Mayun kowacce shekara.
Xi Jinping ya yi kira ga ma’aikatan su inganta nuna jajircewa kan aiki da zama abun misali tare da inganta kwarewar ayyuka.
Ya kuma karfafa musu gwiwar aiki tukuru da aiwatar da kirkire-kirkire, domin samar da ci gaba a fannin zamanantar da kasar Sin da taka muhimmiyar rawa a sabon tafarkin Sin na farfado tare da karfafa kanta.
Har ila yau, ya bukaci kwamitocin JKS da gwamnatoci a dukkan matakai, su kare halaltattun hakkoki da muradun ma’aikata, da taimaka musu shawo kan wahalhalu da matsaloli da inganta samar da kyakkywan yanayi, ta yadda za a rika mutuntawa da girmama ayyuka da ma’aikata. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp