Yau ne, babban sakataren kwamitin kolin JKS Sin Xi Jinping, ya jagoranci taron ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, inda aka yi nazarin halin da ake ciki a fannin tattalin arziki, da tsara ayyukan watanni 6 na karshen wannan shekara.
Taron ya yi nuni da cewa, tun daga farkon shekarar bana, a yayin da duniya ke fuskantar yanayi mai sarkakiya, da ayyuka masu wuyar gaske game da yin kwaskwarima, da raya kasa, da zaman lafiya a cikin gida, kasar Sin ta yi nasarar hada kai wajen kandagarki da dakile yaduwar annobar COVID-19, da raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma, ta kuma samu sakamako mai gamsarwa a aikin kandagarki da dakile yaduwar annobar, tare da samun sabbin nasarori a ci gaban tattalin arziki da zamantakewa.
Taron ya jaddada cewa, ya kamata aikin raya tattalin arziki a watanni 6 na karshen shekara ya mayar da hankali kan kyautata ingantaccen ci gaba, da aiwatar da cikakken tsarin rigakafi, da daidaita tattalin arziki da tabbatar da samun ci gaba mai aminci, da karfafa habakar tattalin arzikin, da daidaita ayyukan yi, farashin kayayyaki, da kiyaye gudanar tattalin arziki a cikin yanayin da ya dace, da kuma kokarin cimma kyakkyawan sakamako.(Ibrahim)