Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya tattauna ta wayar tarho da takwaransa na kasar Cote d’Ivoire, Alassane Ouattara, da yammacin yau Talata.
Yayin ganawar, Xi jinping ya bayyana Cote d’Ivoire a matsayin muhimmiyar abokiyar huldar kasar Sin a Afrika. Ya kuma bayyana cika shekaru 40 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu da za a yi a badi, a matsayin wanda ya cancanci bangarorin biyu su yi murna da shi. Haka kuma, ya ce Sin tana yabawa da yadda Cote d’Ivoire ke rungumar manufar kasar Sin daya tak a duniya, kana a shirye take ta hada kai da Cote d’Ivoire don su ci gaba da goyon bayan juna game da batutuwan da suka shafi muradunsu da zurfafa dangantakarsu zuwa wani sabon matsayi.
A nasa bangare, shugaba Alassane Ouattara, ya ce yana da kyakkyawan fata game da cikar kasashen biyu shekaru 40 da kulla huldar diflomasiyya. A cewarsa, Sin ta taimakawa kasar gaya, kana ta bayar da muhimman gudunmuwa wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya a yankuna da ma duniya baki daya, ciki har da Cote d’Ivoire.
Sannan, tana tallafawa ci gaban tattalin arziki da zamantakewar kasashen Afrika.
Shugaba Ouattara ya kuma jaddada cewa, kasarsa na nacewa ga manufar Sin daya tak, haka kuma tana goyon bayan tsarin huldar kasa da kasa da kuma shawarar Ziri Daya da Hanya Daya.
Bugu da kari, a shirye Cote d’Ivoire take, ta ci gaba da karfafa hadin gwiwa da Sin karkashin tsarin dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afrika na FOCAC, su kara tuntubar juna kan batutuwan yankuna da ma duniya.(Faeza Mustapha)