Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya taya takwaransa na kasar Madagascar Andry Nirina Rajoelina, murnar lashe babban zaben kasar sa. Cikin wani sako da ya aike masa a jiya Talata, shugaba Xi ya taya Rajoelina murnar sake darewa kujerar shugabancin Madagascar.
Ya ce yana dora matukar muhimmanci ga bunkasar alakar Sin da Madagascar, kuma a shirye yake ya yi aiki tare da shugaba Rajoelina, wajen ingiza ci gaban hadin gwiwa daga dukkanin fannoni tsakanin Sin da Madagascar, ta yadda hakan zai amfani al’ummun kasashen 2. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp