Sakatare Janar na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin(JKS) Xi Jinping, ya yi kira ga kwalejojin horar da mambobin JKS da su dage wajen cimma burin kafuwarsu, na horar da kwararru da bayar da gudunmuwar hikimomi ga jam’iyyar.
Xi Jinping wanda shi ne shugaban kasar kuma shugaban hukumar sojin kasar, ya bayyana haka ne a yau Laraba, lokacin da yake jawabi ga taron cika shekaru 90 da kafuwar kwalejin dake karkashin kwamitin kolin JKS da bikin bude sabon zangon karatu na lokacin bazara.