Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi rangadi a biranen Anqing da Hefei na lardin Anhui dake gabashin kasar, da yammacin jiya Alhamis.
Shugaba Xi ya ziyarci unguwar Liuchi ta birnin Tongcheng dake karkashin Anqing da kuma birnin raya harkokin kimiyya na Binhu na Hefei.
- Waiwaye Kan Gudummawar Kasar Sin Game Da Ingiza Hadin Gwiwa Don Bunkasa Shawarar Raya Ci Gaban Duniya
- An Gudanar Da Taron Masanan Kasashen Rukunin Global South A Beijing
Yayin ziyarce-ziyarcen, shugaban ya fahimci kokarin da al’ummomi suke na raya al’adun gargajiya na kasar Sin da raya harkokin da suka shafi al’adu da kabilu, da kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha da gaggauta daukaka ci gaban ayyukan kimiyya da fasaha.
Ya kuma jaddada muhimmancin ci gaba da daukaka akidun al’adun gargajiya na kasar da kara karfafa jituwa tsakanin jama’a da jadadda bukatar sanya kimiyya da fasaha gaba da komai yayin da ake inganta zamanintar da kasar Sin. (Fa’iza Mustapha)