A ranar 7 ga watan Satumba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi tattaki zuwa wani kauye mai suna Longwangmiao na lardin Heilongjiang dake arewa maso gabashin kasar Sin. Xi ya tashi daga Harbin cikin jirgin kasa, fadar mulkin lardin Heilongjiang, daga baya ya hau mota don kaiwa wannan karamin kauye mai mutane dari 5.
A watan Yuli da Agustar bana, yankin arewacin kasar Sin ya gamu da ruwan sama kamar da bakin kwarya wanda fiye da shekaru 100 ba’a yi ambaliyar da ta kai ta muni ba, kuma bala’in ya janyo babbar hasarar rayuka da dukiyoyin al’umma.
A watan Agustar bana, an yi ruwan sama kamar da bakin kwarya da ba’a taba ganin irin karfinsa ba a shekaru 70 da suka gabata a kauyen Longwangmiao, bala’in da ya shafi kusan rabin gonaki da gidaje a kauyen.
A halin yanzu ana himmatuwa wajen aikin sake farfado da kauyen, inda shugaba Xi ya tafi can don ganewa idanunsa yadda ake gudanar da aikin.
Har kullum Xi ya kan maida hankali kan bala’in ambaliyar ruwa, da kula da rayuwar mutanen da bala’in ya shafa. Xi ya bukaci gwamnatoci daga dukkan matakai da su tabbatar da cewa, mutanen da bala’in ya shafa za su fita daga lokacin hunturu ba tare da matsala ba, dalibai kuma za su iya komawa makarantu. Komai kankantar abu, idan zai amfani jama’a, dole ne a yi shi. (Murtala Zhang)