Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta sanar a yau Juma’a cewa, shugaban kasar Xi Jinping zai halarci taron shugabannin kungiyar raya tattalin arzikin ta kasashen Asia da Pasifik (APEC), karo na 32 a Gyeongju na Korea ta Kudu, bisa gayyatar shugaban kasar Lee Jae-myung. Taron zai gudana ne daga ranar 30 ga watan Oktoba zuwa 1 ga watan Nuwamba, kana shugaba Xi Jinping zai yi ziyarar aiki a kasar. (Fa’iza Muhammad Mustapha)













