Bayanai sun tabbatar da rasuwar shugaban kungiyar maharba ta Arewa Maso Gabashin Nijeriya, Muhammad Usman Tola, ranar Talata a Yola.
Wani jigon kungiyar kuma mataimakin mai bada shawara na musamman kan tsaro Yawalem, ya shaida wa LEADERSHIP HAUSA ta waya, cewa marigayin ya rasu ne a asibiti, bayan fama da ciwon ciki.
- Jiga-jigan APC Da Ke Tsammanin Samun Mukamin Siyasa A Gwamnatin Tinubu Sun Shiga Rudani
- Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Rabon Hatsi Tan 42,000
Ya kara da cewa “shugabanmu mutumin kirki, ya rasu yana da shekaru 72, ya bar mata hudu da yaya 13 da jikoki takwas.
“Muna rokon gwamnatin tarayya da ta Adamawa da kada a dauko wani da wani a dora mana a matsayin shugaba, ya kamata a bar mu mu zabi wanda ya dace da mu, domin kada a samu matsala a aikinmu na tsaro” in ji Yawalem.
Tarihi dai ba zai mance da muhimmiyar gudumuwar da marigayi Tola da kungiyar maharba suka bayar a yaki da ‘yan kungiyar Boko Haram da masu aikata miyagun ayyuka a jihohin Arewa Maso Gabas ba.