Majalisar Wakilai, ta gaggauta janye wani kudiri da aka gabatar a gabanta wanda ya bukaci daurin shekaru biyar zuwa 10 ga duk wani dan Nijeriya da ya ki rera taken kasa.
Janye kudirin ya biyo bayan suka daga bangarori da dama, musamman fusatattun matasan da ke jin radadin kuncin rayuwa.
- An Kaddamar Da Dandalin Bunkasa Noma Da Yaki Da Fatara Na Sin Da Afirka A Kenya
- Ambaliyar Ruwa: Mutane 16 Sun Rasu, 3,936 Sun Rasa Matsugunansu A Jigawa – SEMA
Shugaban majalisar wakilai Tajudeen Abbas da kansa ya gabatar da kudirin, wanda ya kai ga karatu na biyu kafin janye shi.
Dokar kuma ta bukaci daurin duk wani wanda aka samu da laifin lalata wani abu mai dauke da alamun kasa ko kuma wajen ibada ko kuma tunzira jama’a yin tashin hankali.
Kudirin, ya ce duk wani wanda ya tare hanyar jama’a ko ya karkata hanyar jama’a ba tare da izini ba ko kuma hana jama’a fita daga gidajensu ba bisa ka’ida ko kuwa shirya zanga zanga ba tare da izini ba, zai biya tarar Naira miliyan biyu ko daurin shekaru biyar ko kuma duka biyun.
Mai magana da yawun shugaban majalisar, Musa Abdullahi Karshi ne, ya sanar da janye kudirin dokar saboda fushin jama’ar kasa.
‘Yan Najeriya da dama na nuna fushinsu ga gwamnati dangane da tsadar rayuwar da ta haifar da zanga-zanga a baya-bayan nan.