Shugaban majalisar dokokin kasar Fiji Filimone Jitoko, ya ce yadda kasar Sin ta samar da nagartattun manufofi, da samun nasarar kawar da fatara, da inganta tsarin dimokradiyya, ta yadda za ta shafi dukkan bangarorin zaman al’umma, sun kasance abin koyi ga kasarsa.
Filimone Jitoko, ya bayyana hakan ne kwanan nan yayin zantawarsa da wata wakiliyar CMG a birnin Beijing, lokacin da ya ziyarci kasar Sin a karon farko, inda ya ce ziyarar ta ba shi damar samun karin ilimi, da kuma yin tunani mai zurfi.
Ya kara da cewa, kasar Fiji na godiya ga kasar Sin bisa yadda take fahimtar bukatun kananan tsibiran dake yankin tekun Pasifik ta fuskar tinkarar sauyin yanayi, kuma Fiji na fatan zurfafa hadin gwiwa da kasar Sin a fannoni da dama, kamar na aikin gona, da kamun kifi, da kayayyakin more rayuwa, da gina hanyoyi, da dai sauransu. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp