Sakamakon alfarmar watan Ramadan, shugaban Majisar Dattawan Nijeriya, Sanata Ahmed Lawan, ya biyawa daurarru 15 ba shi a gidan gyaran hali a da ke garin Gashu’a, shalkwatar karamar hukumar Bade ta jihar Yobe.
Wadanda suka ci gajiyar afuwar, bayan yanke musu hukuncin zaman gidan gyaran hali na shekaru daban-daban, sakamakon bashin da ake bin su, daga kananan hukumomin Yusufari mutum 4, Jakosko mutum 3, yayin da sauran suka fito daga Potiskum da Bursari a jihar Yobe.
- Babu Batun Bayyana Sakamakon Zabe Ta Na’ura A Cikin Dokar Zabe –Lawan
- Yanzu-yanzu: Sanata Ahmed Lawan Ya Lashe Mazabarsa A Yobe Ta Arewa
Baya ga haka kuma, Sanata Ahmed Lawan ya bai wa kowane daya daga cikin su kyautar naira 50,000 da yadin shadda 10 domin su koma cikin iyalin su tare da gudanar da ayyukan ibadar watan Ramadan.
Da yake jawabi a madadin Shugaban Majisar Dattawan, shugaban karamar hukumar Bade, Mallam Ibrahim Babagana, ya ce, sun gudanar da wannan aikin jinkan ne bisa umurnin, Sanata Ahmed Lawan, ga mutanen da dukan su bashi ne ya kai su gidan gyaran hali.
“Duk da ba iya adadin da ya bamu umurnin a yi wa afuwar ba, ya ce mu biyawa wadanda ake bi bashin amma sauran laifukan ba zai tsoma baki a kai ba.
Hon. Babagana ya kara da cewa, “Akalla ya kashe sama da naira miliyan 3 wajen yanto wadannan mutanen kuma ya tallafa wa kowane mutum daya da kyautar naira 50,000 da yadin shadda 10. Mu na yi masa addu’ar Allah ya saka masa da alheri.”
Tuni dai wadannan mutane suka kama hanyar komawa cikin iyalinsu tare da bayyana matukar farinciki da godiya ga shugaban Majisar Dattawa.