Babban sakatare na Majalisar Dinkin Duniya MDD, Antonio Guterres ya yi kakkausar martani inda ya yi Allah wadai game da yunkurin juyin mulki a kasar Nijar.
Rahotanni sun bayyana cewa, sojoji masu gadin fadar shugaban kasa, sun tsare shugaba Mohamed Bazoum da iyalansa a gidansa da ke Yamai babban birnin kasar a ranar Laraba.
Wannan yunkuri, ya kai ga Shugaban Hukumar Tarayyar Afirka da ECOWAS, ta bayyana abin da suka yi a matsayin “yunkurin shirin juyin mulki” – ko da yake ba a samu rahotonnin harbe-harbe ba.
Rahotanni sun ce, jami’an da suka yi wannan yunkurin, ba su samu goyon bayan sojoji ko jami’an tsaro ba amma tattaunawar da aka yi don ganin an sako shugaba Bazoum ba ta yi nasara ba har ya zuwa yanzu.
Guterres, Ya yi Allah-wadai da kakkausar murya ga duk wani yunkuri na kwace mulki da karfin tsiya da kuma kawo cikas ga mulkin ddimokuradiyya, zaman lafiya da kwanciyar hankali a Nijar.
Babban sakataren ya yi kira ga duk masu ruwa da tsaki da abin ya shafa da su yi duk mai yiwuwa don tabbatar da tsarin dimokuradiyya a kasar.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce za ta kasance tare da gwamnati da al’ummar Nijar a koda yaushe.