Kwanan baya shugaban kasar Mongoliya Ukhnaagiin Khurelsuh ya zanta da wakilin CMG, inda ya bayyana cewa, zai yi kokari domin ingiza hadin gwiwar dake tsakanin kasarsa da kasar Sin bisa shawarar ziri daya da hanya daya da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar, da tsare-tsaren raya kasarsa na “hanyar filin ciyayi”.
Shugaba Khurelsuh ya yi tsokaci cewa, lamari zai sa kaimi kan ci gaban huldar dake tsakanin kasashen biyu, kuma zai ingiza ci gaban yankin gaba, tare kuma da ba da gudummowa kan cimma babban burin da kasashen Sin da Mongoliya suka gabatar.
Ya kara da cewa, har kullum Mongoliya tana goyon bayan shawarar ziri daya da hanya daya, kuma tana son inganta hadin gwiwar sassa daban daban bisa shawarar.
Haka zalika, yayin taron shugabannin kasashe mambobin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai karo na 22 da aka kira a watan Satumban shekarar 2022, shugabanin kasashen Mongoliya da Sin da Rasha sun yin ganawa tsakaninsu, inda suka cimma matsaya kan yadda za su karfafa hadin gwiwa a fannoni daban daban. (Mai fassarawa: Jamila)