A bana ne ake cika shekaru 20 da kaddamar da ka’idar “tsaunuka biyu” wadda shugaba Xi Jinping ya gabatar, inda ya ambaci ruwa mai tsafta da tsaunuka masu kima, a matsayin kadarori masu daraja da za a kwatanta su da zinariya da azurfa. A kwanakin baya, shugaban kasar Mozambique Daniel Francisco Chapo, ya bayyanawa wakilin gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG cewa, ya mika sakonsa na taya Sin murnar cimma nasarori bisa manufar “tsaunuka biyu” a kasar Sin.
Shugaba Chapo, ya yi nuni da cewa, Mozambique ita ma tana da yankunan kiyaye muhallin halittu, da yankunan gandun dabbobi, wadanda suka sa kaimi ga sha’anin yawon shakatawa a wurin. Don haka, ya nuna goyon baya ga kiyaye muhalli, wanda ya ce batu ne mai babbar ma’ana.
Haka zalika kuma, shugaba Chapo ya amince da manufar da shugaba Xi Jinping ya gabatar. Ya yi imanin cewa, manufar “tsaunuka biyu” za ta ci gaba da samun kyakkyawar makoma. Ya kamata kasar Mozambique da sauran kasashen duniya, su bi wannan manufa da kiyaye muhalli tare. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp