Yanzu haka ana ci gaba da gudanar da taron koli na dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC na shekarar 2024 a nan birnin Beijing. Shugaban kasar Namibia Nangolo Mbumba ya bayyanawa wakilin babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG cewa, batun bunkasuwa yana da nasaba da kasar Sin.
Shugaba Mbumba ya bayyana cewa, Sin abokiyar hadin gwiwa ce, kuma kasarsa da Sin suna sada zumunta a tsawon lokaci. Kaza lika kasarsa ta samu moriya da dama, yayin da ake gudanar da hadin gwiwa a tsakanin Afirka da Sin. Ya ce, ya kamata kasashen Afirka da Sin su yi kokarin samar da yanayi na zaman lafiya da na karko a duniya, da sa kaimi ga samun bunkasuwa tare, don kawo wa jama’ar duniya hakikanin wadata.
Game da dandalin FOCAC, shugaba Mbumba ya bayyana cewa, dandalin FOCAC ba ma kawai dandali ne na mu’amala cikin sauri ba, har ma ya sa kaimi ga jama’ar kasarsa Namibia da bangaren Sin, suna ta samun moriya da sada zumunta. (Zainab Zhang)