Shugaban Nijeriya Bola Tinubu, ya aza harsashin ginin sabuwar tashar samar da lantarki daga gas, wanda kamfanin China Machinery Engineering Corporation zai gudanar.
Da yake jawabi yayin bikin da ya gudana jiya Jumaāa, shugaba Tinubu ya bayyana tashar mai zaman kanta ta Gwagwalada, a matsayin mai matukar muhimmanci ga kasar mafi yawan alāumma a Afrika, haka kuma wani babban mataki a kokarin gwamnati na kafa bangaren makamashi mai karfi da zai iya bunkasa tattalin arzikin kasar.
Ya ce Nijeriya ba za ta iya zama mai samar da kayayyaki da karfin masanaāantu ba, kuma ba za ta iya shawo kan talauci ko samar da ayyukan yi masu samar da kudin shiga mai yawa a bangaren samar da kayayyaki ba, har sai ta iya nema da samarwa da raba wutar lantarki da za a iya dogaro da shi.
A nasa bangare Cui Jianchun, jakadan kasar Sin a Nijeriya, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, tashar za ta taka muhimmiyar rawa wajen taimakawa Nijeriya cike gibin da take da shi ta fuskar samar da lantarki. Ya ce bayan kammaluwarta, ana sa ran tashar za ta cimma bukatun lantarki na babban birnin kasar da yankunan dake kewayensa.
Aikin tashar wadda za ta samar da lantarki daga jerin makamashin, zai gudana ne mataki-mataki, inda za a kammala mataki na farko mai megawatt 350, shekaru 3 bayan kaddamar da aikin. (Faāiza Mustapha)