Shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta Ƙasa, Isah Jere Idris ya sanar da ƙarin girma ga jami’an hukumar su 4,526 da suka yi jarrabawar ƙarin girma da waɗanda suka samu horaswa daban-daban ta ɗaga darajar muƙami a shekarar 2021.
Tabbatar da ƙarin girman na ƙunshe ne a cikin wasiƙar da ta zo daga Hukumar Gudanarwar Rundunonin da ke ƙarƙashin Ma’aikatar Cikin Gida da aka yi wa lambar CDCFIB/S.33/VOLIII/54 mai ɗauke da kwanan wata,18 ga Agusta, 2022.

Shugaban hukumar ya bayyana hakan ne a yau a hedikwatarta yayin da yake yi wa wasu jami’ai masu taimaka masa da ke cikin ma’aikatan da aka yi wa ƙarin girma ado da sabbin muƙamansu.

Sanarwar da ta fito daga Jami’in hulɗa da jama’a na NIS, wanda shi ma aka ƙara masa girma daga ƙaramin Mataimakin Kwanturola (ACI) zuwa Babban Mataimakin kwanturola (DCI), Amos Okpu, ta ce jami’ai masu muƙamin ƙaramin mataimakan Kwanturola 145 sun samu ƙarin girma zuwa Babban Mataimakin Kwanturolan Shige da Fice; sannan masu muƙamin Babban Sufiritanda 99 sun samu ƙarin girma zuwa ƙaramin mataimakin Kwanturola.
Bugu da ƙari, akwai masu muƙamin Sufiritanda 307 da aka mayar da su matsayin Babban Sufiritanda; kana mataimakan Sufiritanda 338 sun samu ci gaba zuwa matsayin Sufiritanda.

Sauran waɗanda suka samu ƙarin girman su ne jami’ai 589 da aka ciyar da su gaba zuwa muƙamin mataimakin Sufiritanda na ɗaya (I), sai wasu 794 da aka ƙara musu muƙami zuwa Mataimakan Sufiritanda na biyu (II).
Har ila yau takardar ta yi bayanin cewa,
jami’ai masu muƙamin Sufeto 21 sun samu ci gaba zuwa mataimakin Sufiritanda na biyu (II). Yayin da wasu jami’ai 1254 suka sami ci gaba zuwa matsayi na Mataimakin Sufeto na biyu (II), kana akwai jimillar ƙananan jami’ai 979 da suka samu ƙwarewar aiki da aka ɗaga darajarsu zuwa matsayi na Mataimakin Sufiritanda na biyu.

Da yake jawabi a wajen bikin adonta muƙarrabansa, Shugaban NIS CGI Isah Jere Idris ya yaba wa Ministan Harkokin Cikin Gida, Ogbeni Rauf Aregbesola wanda kuma ya zama shugaban hukumar gudanarwar rundunonin da ke ƙarƙashin ma’aikatar bisa jajircewarsa wajen ciyar da ma’aikata gaba.
Ya bukaci sabbin jami’an da aka kara musu girma da su ƙara ƙwazo da saka karamcin da aka yi musu ta hanyar sadaukarwa da kuma biyayya a bakin aiki.
Ya kuma bai wa gwamnati tabbacin cewa hukumar a ƙarƙashinsa za ta ci gaba da bayar da gudunmawa mai amfani ga zaman lafiya da ci gaban kasa.

Daga cikin jami’an da aka yi wa ado da sabbin mukamansu akwai Jami’in hulɗa da jama’a na NIS Amos OKPU, wanda aka ƙara wa girma zuwa DCI; da Jami’in kula da tsare-tsare na Kwanturola Janar MY Dutse mai barin gado da magajinsa MA Ajimobi wanda a yanzu suka zama Manyan Mataimakan Kwanturola.

Sauran sun haɗa da Mercy Gadzama, Manajar Kula da Cibiyar Fasaha ta NIS, da a yanzu ta zama Babbar Sufiritanda, da Jami’in Tsaro na Kwanturola Janar AO Olukoya, da aka kara masa girma zuwa muƙamin Babban Sufiritanda da Tanko Godiya da Nguar Loice Titus na Sashen Kai Ɗaukin Gaggawa (RRS), duka biyu da aka ƙara musu girma zuwa mataimakan Sufiritanda na Shige da Fice (II).
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp