Yayin da shugaban kasar Saliyo Julius Maada Bio yake hira da wakilin babban gidan rediyo da telebijin na kasar Sin wato CMG a kwanakin baya, ya bayyana cewa, kasar Saliyo tana son koyon fasahohin Sin da fahimtar basirar Sin ta samun ci gaba cikin sauri.
Shugaba Bio ya bayyana cewa, a yayin ziyararsa a kasar Sin, yadda mutanen Sin suke yi wa kansu iyaka, ya burge shi sosai. A ganinsa, wannan ita ce alamar kokarin neman ci gaba.
Ban da wannan kuma, shugaba Bio ya yi nuni da cewa, dalilin da ya sa kasar Sin ta samu nasarori a halin yanzu, shi ne Sin ta dauki matakan neman ci gaba masu dacewa. Manufar zamanintarwa iri ta kasar Sin ta samar da hanya ko shiri ga kasashe masu tasowa wajen samun ci gaba da kansu. Ya ce yana son kasarsa ta Saliyo ta bi hanyar kasar Sin da fahimtar basirar Sin ta samun ci gaba cikin sauri. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp