Shugaban kasar Serbia, Aleksandar Vucic, ya yi hira da ‘yar jaridar babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG a kwanan nan. Yayin da aka ambaci ziyarar aiki da shugaban kasar Sin Xi Jinping zai kai kasar Serbia, Vucic ya ce, yana fatan ganawa da shugaba Xi Jinping, ziyarar nan zai kawo damammaki masu kyau ga al’ummar Serbia.
Vucic ya bayanna cewa, a ganinsa, shugaba Xi Jinping yana da kirki, zai cika dukkanin alkawuransa. Kasar Serbia tana farin ciki sosai wajen shiga aikin gina shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya tare.
- Xi Ya Aike Da Sakon Taya Murna Ga Taron OIC Karo Na 15
- Sin Ta Harba Na’urar Chang’e-6 Domin Kwaso Samfura Daga Bangaren Duniyar Wata Mafi Nisa
Kazalika, jimillar cikinikkayar dake tsakanin kasashen Serbia da Sin ya riga ya kai dalar Amurka biliyan 6.1, kuma yarjejeniyar gudanar da cinikayya cikin ‘yanci da kasashen biyu suka sa hannu za ta sanya jimillar cinikayyar bangarorin biyu ta ninka sau 2 ko sau 3 bisa yadda take a halin yanzu a cikin shekaru 10 masu zuwa.
Vucic ya kara da cewa, shugaba Xi shugaba ne da ya ba da gudummawa wajen daina yaki da kafa zaman lafiya na dogon lokaci. Ya yi kira ga saura da su ji shawarwarin shugaba Xi, su yi sasantawa don cimma matsaya daya, saboda a karshe dai abin da ya shafi bil’adama shi ne zaman lafiya da kwanciyar hankali.(Safiyah Ma)