A kwanan nan ne wata wakiliyar CMG, wato babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin, ta samu damar zantawa da shugaban kasar Seychelles, Wavel Ramkalawan, wanda ya ce raya shawarar “ziri daya da hanya daya” cikin hadin-gwiwa, na da makoma mai haske, kuma mai dorewa. Shugaba Ramkalawan, ya kuma bayyana fatansa na zuwan lokacin taron kolin dandalin tattauna hadin-kan Sin da Afirka wato FOCAC, wanda ke tafe a watan Satumbar bana a Beijing, fadar mulkin kasar Sin.
Ya ce sana’ar yawon bude ido, wadda ita ce ginshikin ci gaban kasarsa, ta samu koma baya mai muni a lokacin yaduwar cutar numfashi ta COVID-19, a hannu guda kasashen yammacin duniya sun ayyana Seychelles a matsayin kasa mai arziki, don haka ta kasa samun rancen kudi mai rahusa daga kasashen yammacin duniya, kafin kasar Sin ta samar wa Seychelles din tallafi bisa zumuncinsu.
- Jami’in Kenya: Taron Dandalin FOCAC Zai Zurfafa Dangantakar Sin Da Kenya
- An Kaddamar Da Dandalin Bunkasa Noma Da Yaki Da Fatara Na Sin Da Afirka A Kenya
Yayin da ya tabo batun raya shawarar “ziri daya da hanya daya” cikin hadin-gwiwa, shugaban na Seychelles ya ce, lokacin da ake aiwatar da hadin-gwiwa a wannan fanni, kasar Sin ba ta taba nuna girman kai ba, kana, ba ta taba matsawa Seychelles ba, maimakon haka kasashen biyu sun yi hadin-gwiwa bisa tushen mutunta juna. Kuma a cewarsa, raya shawarar cikin hadin-gwiwa, na da makoma mai haske kuma mai dorewa, kana makoma ce dake kunshe da hadin-gwiwar bangarori daban-daban.
Har wa yau, game da taron kolin dandalin FOCAC wanda zai gudana a watan Satumbar bana a Beijing, shugaban Seychelles ya yi fatan samun nasarori a wajen taron, inda ya ce Seychelles da Sin, sun riga sun kulla dangantakar hadin-gwiwa mai karfi tsakaninsu. Ya kuma yi fatan dangantakar abokantaka tsakanin kasashen biyu za ta ci gaba da bunkasa. (Murtala Zhang)