Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Timor-Leste Jose Ramos-Horta da firaministar kasar Italiya Giorgia Meloni wadanda suke ziyarar aiki a birnin Beijing, fadar mulkin Sin, a yau Litinin daya bayan daya.
Lokacin da yake ganawa da Jose Ramos-Horta, shugaban kasar Timor-Leste, Xi Jinping ya ce, kasar Sin a shirye take ta karfafa alaka da dabarun raya kasa da kasar Timor-Leste, da kuma taimaka mata wajen samun ‘yancin kai na tattalin arziki da bunkasuwa a fannoni daban daban.
- Wang Yi Ya Bayyana Matsayin Kasar Sin Kan Batun Tekun Kudancin Kasar
- Sin Da Amurka Sun Amince Da Ci Gaba Da Tuntubar Juna A Dukkanin Matakai
A nasa bangare, Ramos-Horta ya ce, Timor-Leste yana goyon bayan duk kokarin da kasar Sin ke yi na kare ikon mallakar kasa da cikakken yankinta.
Bayan tattaunawar, shugabannin kasashen biyu sun shaida rattaba hannu kan shirin hadin gwiwa kan aikin gina “shawarar ziri daya da hanya daya” tare da wasu takardun hadin gwiwar kasashen biyu a fannonin aikin gona, da kiyaye muhalli, da tattalin arzikin dijital, sufurin jiragen sama, da dai sauransu, bangarorin biyu sun fitar da “sanarwar hadin gwiwa na jamhuriyar jama’ar kasar Sin da jamhuriyar dimokaradiyyar Timor-Leste kan zurfafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare”.
Sannan a lokacin da yake tattaunawa da firaministar kasar Italiya Giorgia Meloni, shugaba Xi, ya ce kasarsa da Italiya na kan iyakokin karshe na tsohuwar hanyar siliki, kuma kawancen musamman na tsawon lokaci tsakanin kasashen biyu ya samar da babbar gudummawa ga daukacin musaya, da koyi da juna tsakanin wayewar kan gabashi da yammacin duniya, tare da tallafawa ci gaban bil adama.
Shugaban na Sin ya kara da cewa, ruhin hanyar siliki na zaman lafiya da hadin gwiwa, da yin komai a bude, da tafiya tare da dukkanin sassa, da koyi da juna, da cimma moriyar juna, sun kasance wata haja mai kima da Sin da Italiya suka raba tsakanin su.
Daga nan shugaba Xi ya ce kamata ya yi sassan biyu su goyi baya, da yayata ruhin hanyar siliki, su nazarci tare da bunkasa alakar dake tsakanin su ta mahangar tarihi, da burin cimma nasara ta tsawon lokaci, tare da ingiza alakar su bisa daidaito. (Mohammed Yahaya, Saminu Alhassan)