Rahotanni sun bayyana cewa, fitaccen kwamandan ‘yan ta’adda Bello Turji ya mika wuya tare da sako wasu mutane 32 da aka yi garkuwa da su, biyo bayan wani shirin zaman lafiya da malaman addinin musulunci suka yi a jihar Zamfara.
Wani fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, Musa Yusuf, wanda aka fi sani da Asadus-Sunnah ne ya bayyana hakan yayin wani taron addini da aka yi a ranar Litinin a Kaduna.
- LASTMA Ta Rufe Gidan Casu A Legas Saboda Karya Dokar Hanya
- BUA Siminti Ya Ƙaddamar Da Shirin Horas Da Matasan Sakkwato
A cewar Asadus-Sunnah, wannan nasarar ta biyo bayan wasu tarurrukan da aka gudanar a watan Yuli tsakanin malamai da wakilan Turji a dajin Fakai, dake karamar hukumar Shinkafi a jihar Zamfara.
“Mun gana da Turji, Dan Bakkolo, Black, Kanawa da Malam Ila, wadannan su ne kwamandojin ‘yan bindiga dake addabar yankunan, kuma dukkansu sun amince da shawarwarin zaman lafiya,” in ji Yusuf.
Ya bayyana cewa, mazauna Shinkafi ne suka gayyace su, inda suka nemi a taimaka musu wajen ganin sun samu damar zuwa gonakinsu da suka dade suna karkashin ikon ‘yan bindigar.
Ya ce, za a mika makaman ne a matakai uku, inda su koma ‘yan bindigar suka bar manoman yankin su koma gonakinsu da ke tsallakin rafin wanda hanya ce zuwa ga yankin Turji.
“Turji ya kuma saki fursunoni 32 da aka yi garkuwa da su a matsayin wani bangare na yarjejeniyar zaman lafiya,” in ji Yusuf yayin da yake nuna faifan bidiyo na wadanda aka ceton yayin da suke barin sansanin Turji acikin mawuyacin hali.
Daga cikin wadanda aka ceto har da mata da kananan yara, wadanda wasunsu sun shafe kusan watanni hudu a hannunsu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp