• English
  • Business News
Sunday, September 14, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shugabanci A Nijeriya: A Ina Ne Gizo Ke Saƙar?

by Muktar Anwar
3 hours ago
in Manyan Labarai
0
Shugabanci A Nijeriya: A Ina Ne Gizo Ke Saƙar?
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Kalmar shugabanci na daga sanannu kuma wasu shahararrun kalmomi da aka saba ji dare da rana, kaka da kakanni. Kalma ce mai saukin ji, ko fada, sai dai wajen aikatata a aikace, lamarinta kan gagari kundila.

A Nijeriyar jiya da yau, kowa na da burin a yabi nasa, koko shi a kankin-kansa a yaba masa, yayinda suke bisa kujerar shugabanci, ko bayan saukarsu. Kowace kabila yau cikin Nijeriya, na da irin nasu gwarzayen shugabannin da kwata-kwata tarihi bai da karfin gaban da zai sanya sunayensu cikin kwandon shara!!!.

  • An Cafke Bature Ɗan Shekara 37 Kan Mutuwar Ɗan Nijeriya Mazaunin Birtaniya
  • Madabba’ar Sin Ta Ba Da Gudunmuwar Littattafai Ga Makarantun Koyar Da Sinanci A Nijeriya

Ba ya ga mabanbantan ɓangarori da kabilun Kasar da kowa cikinsu gwani ne wajen kare irin shugabanninsu na-dauri, haka ma abin yake ga mabiya addinai iri daban-daban a Kasar. Sai dai ga dukkan alamu, kabilun wannan Kasa da mabiya addinansu na wannan lokaci, ba a shirye ne suke ba, wajen bin sawun magabatansu na kwarai. A kullum, sai dai kawai a ɓuge ne da yabon magabata daga tsoffin jagorori ko a ce shugabannin Kasar. Kawai, a na furtawa ne a baki, kuma ba a shirye ake na aikata irin kyawawan aiyukan wadancan shugabannin da ake ta kan kururuta aiyukansu dare da rana ba.

 

Ta Yaya Yabon Fatar-baki Zai Haifar Da Shugabanci Nagari A Kasa?

Labarai Masu Nasaba

Sojoji Sun Ceto Mutane 30 Da Aka Yi Garkuwa Da Su, Sun Kashe ‘Yan Ta’adda Da Dama

Dawowa Hutu Ya Tayar Da Hankalin Iyaye Saboda Ƙarin Kuɗin Makaranta

Sama da kashi casa’in (90%) na kabilu da mabiya addinai da ke raye cikin Nijeriyar yau, ba su damu da samar da shugabanci nagari cikin Kasar ba a aikace, sai dai kawai a mafarkance. Za a iya gane hakan ne ta hanyar nazartar aiyukansu hada da furuce-furucensu!!!.

Da daman mutane ba sa zaɓar wani kansila da zuciya guda, sai don ya dare kujerar ne ya biya musu bukatunsu na daidaiku. Haka Ciyaman, haka “yan Majalisun jiha, haka Gwamna, haka” yan Majalisun taraiya, haka ma kujerar Shugaban Kasa. A tunanin akasarin mutane a yau, bukatunsu na daidaiku, shi ne mazaɓa, shi ne karamar hukuma, shi ne jiha, kai, kacokan ma shi ne Nijeriya. Saboda haka, wajen samun biyan wadancan bukatu, komai na iya faruwa, a duk sa’adda wani lamari ya tasamma zame musu wani tsaiko, a kan hanyarsu ta cimma irin wadancan bukatu ko muradai, sawa’un, masu kyau ne ko gurɓatattu.

Irin wadancan halaye na bukatar-kai linzami, shi ne mafi munin ta’adar da ke kange kowace irin nahiya ko kasa a Duniya daga samun ci gaba. Da Ciyaman ba shi da hali irin na bukatar-kai linzami, da tuntuni dubban daruruwan jama’ar karamar hukumarsa sun jima da tsallake mummunan kangin wahalar rayuwar da suke ciki tsundum a yau. Ta fuskar sama musu aiyukan-yi na hakika tare da tallafarsu zuwa ga samun jari da sauran samun damarmaki a rayuwa. Sai suka gwammace su hade kai da baki da gwamna da sauran “yan majalisu, wajen yin wa-kaci ka-tashi da dimbin miliyoyin kudaden da aka rantsar da shi cewa zai kare su. Amma sai aka wayigari son-kai da son-zuciya sun maishe su rakuma da akala.

Babu aiyukan-yi kwarara a kananan hukumomin nasu, sun gaza yi wa gwamna tsayuwar-gwamin-jaki wajen kare muradun al’umarsu, amma a duk inda aka je aka zo, sai a samu cewa talakawa raunane ke dandana kudarsu dare da rana, amma ba Ciyaman ba, kuma ba Gwamna ba. Duk inda gwamnoni za su kai ga rike kudaden majalisun kananan hukumomi, ciyaman ya fi karfin ci da sha, mallakar gida, harkar lafiya, duka da shi da iyalansa. Ke nan, da gwamna da ciyaman, likkafar rayuwarsu ta ci gaba, sauran mutane ne aka yasar a tasha.

Tuntuni cikin wannan Kasa, jagoranci da shugabancin da ake gudanarwa a matakan jihohi da can matakin gwamnatin taraiya suka gurɓace. Gwamnoni nawa ne a Kasar, bayan sun zubar da hawaye game da aiyukan “yan ta’adda a jihohinsu, aka ji, ko aka ga, sun sauka daga kan kujerunsu, don ba da dama ga wasu mutanen da za su iya maye gurbinsu tare da murkushe tarnakin ” yan ta’addar sama da su?. Kawai sai dai a ga gwamna na zub da hawaye tare da damke kujerersa kamkam tamkar nonon uwa. Babu shakka akwai duk wani nau’i na yaudara cikin wannan surkullen gajiyawa da gwamnoni ke yi dare da rana. Sannan, a duka cikin kudanci da arewacin Kasar akwai irin wadancan gwamnoni, wadanda suka yi likimo bisa kujerun mulkin tamkar na gado.

Ba gwamna kawai ba, hatta akasarin kwamishinoni da ke karkashin gwamnoni, sun fi mayar da hankali ne, ta yaya lalitarsu za ta cika ta batse?. Gwamnoni sun aza su bisa kujerunsu ne kadai, don su dafa musu wajen samar da shugabanci nagari a matakan jihohi, sai dai, tsawon lokaci kwalliya ta gaza biyan kudin sabulu!!!. A kullum kalaman da ke fitowa daga bakunan kwamishinonin, ba ya wuce cewa, mai girma gwamna fa ya ki sakin kudade ga masana’antun nasu. Duk da haka, daga lokacin da wata jam’iyyar adawa ta amshe mulkin jihar, sai a ji sama da miliyan dubu na naira, sun yi ɓatan-dabo daga ofishin Hon. Kwamishina.

An dauki lokaci, ba tare da samun gudanar da shugabanci abin koyi daga jerin irin wadancan kwamishinoni. Idan gwamna ya nada ka aiki, sai ya hana ka kudaden gudanar da aiyuka, mene ne alfanun ci gaba da aiki a karkashinsa ga al’umar jiha?. Sai dai da yake, a na raɓar gwamna ne don cimma bukatar kashi-kai linzami, sai Mr Kwamishina ya ci gaba da nanikar gwamna, ko babu komai, ba zai rasa ci da sha da sauran bukatun rayuwa har zuwa saukarsu daga kujerun mulki. Ke nan, akwai yawo da hankali a ji kwamishina na cewa, gwamna ya ki sakin kayan aiki. Uzurin rashin sakin kayan aiki, ka iya karɓuwa, muddin gwamnatin na kasa da Watanni shida (6) ne bisa karagar mulki. Saɓanin haka akwai ayar tambaya (?)

Babu shakka, mu na wani lokaci ne da mutum zai hanga gabas da yamma kudu da arewacin Nijeriya, sai ya gajiya wajen samun sahihan mutanen da shugabanci na adalci ke maraba da su. Sai lamuran ke neman zama tamkar kowane gauta… tattare da manyan kabilun Kasar  uku, gurɓatattun shugabannin cikinsu, sun ninka nagartattun cikinsu sau malala gashin tinkiya. Alhali, a can baya, kowannensu na da sahihan mutane nagartattu, abin koyi, wajen iya tafiyar da shugabancin da yai hannun riga da hadama da zalama, saɓanin yanzu.

Sai aka wayigari, hadamammun shugabanni hatta a kungiyar masu sana’ar shayi ko sayar da masara, sune a kullum aka tsaya zaɓe ke lashewa, su ke da kudaden badawa a matsayin cin-hanci, don su ci gaba da dauwama bisa kujerun shugabancin da babu fansho ko giratuti tattare da su. Son zuciya da zarmewar, game da mugun son shugabanci tare da rashin ba da hakkinsa, lamarin ya wuce batun kungiyoyin Siyasa da masu sayar da Shayi, hatta cikin rigar Addini ma lamura sun yi gurɓatar da ake zare manyan bindigogi a na kashe kai, da sunan a na bisa tafarki. Me ke faruwa da batun masu ikirarin jihadi a gabashin arewacin wannan Kasa?

Me ke faruwa a Maidugiri da Yobe a yau? Da yawan mabiyansu na yin ribas, tare da mika wuya ga rundunar Sojojin Nijeriya, tamkar irin yadda manyan “yan Siyasa da kanana ke yin hijirar canja jam’iyya, daga A zuwa B, ko daga C zuwa D. Suma rukunin “yan ta’adda ba a bar su ba a baya, wajen gudanarwa da mutanensu gurɓataccen shugabanci, hakan ke zama silar yi wa jagororinsu gadar zare, tare da rufta su ciki, irin yadda Sojojin Niger suka yi wa shugaba Baazou!

Ta Ina Ne Za A Gyatta Lamarin Shugabancin?

Daga kan shugaban Kasa ne za a faro gyaran, ko kuwa daga kan kujerar Kansila?. Koko daga limaman Masallatai ko na Coci-coci?. Daga jagororin Kotu kotu ne za a fara gyaran, koko daga kamfanin wutar lantarki?. Daga jagororin tsaro ne gyaran zai fara, koko daga shugabannin tasha ko na kasuwanni?. Koko uwa uba, za a faro gyaran ne daga ɓangaren jagorancin Miji da Mata a gida?. Sai aka wayigari a Nijeriyar yau, mutum ba shi iya bugun kirji ya yi nuni zuwa ga nagartaccen shugabanci daga jerin rukunin wadannan mutane! Ta yaya ne za a ga daidai?. Ta kai ta kawo, hatta a shugabancin manyan makarantun ilmi na Kasar, Farfesa kan yi rub da ciki bisa lalitar tsangaya. Sune fa ke kyankyashe sabbin zubin shugabannin Kasar a nan gaba, amma sai ga laya na gardamar kin kyawon rufi.

Sai ga mutane an bazama daji, an kasa gano bakin-zaren. Wace jam’iyyar siyasa ce a yau cikin Kasar ba ta da gurɓatattun shugabanni? Idan ba ka sani ba, to jira lokaci Malam Zurƙe. Na daga rashin sanin alkiblar sahihan jagorori, mutum kan dauki lokaci tare da wanke ko tsarkake wani shugaba nasa, ba abin mamaki ne ba, zuwa wani lokaci, a ji shi, yana antaya bakaken kalamai ga wannan tsohon jagora nasa!. Hatta shugabancin kungiyar Kwadago ta Kasa, NLC, bai suɓuce daga samun zarge-zarge ba. A lokaci guda, suma za a same su ne suna masu ta-da-jijiyar wuya ga wani shugabanci na daban, tare da wanke nasu da ruwan alkausara.

Bukatar Komawa Bisa Sirdi

Na’am, gyaruwar wani shugabanci kan zama silar gyaruwar wasu rukunin shugabancin. Gyaruwar shugabancin malaman addini da na masu mulki, na iya zama a sawun gaba, wajen muhimmanci, sai dai hatta suma, shugabancin gida, na tsakanin miji da mata, kan iya samar da kyakkyawan sakamako ga wadannan shugabanci biyu (na masu mulki da na maluma). Kuma gurbacewarsa kan iya taka muhimmiyar rawa wajen gurɓacewarsu.

Yayinda aka tasamma samar da nagartaccen shugabanci a kasa, kowane nau’in shugabanci, daga kowane rukunin jama’a, kan iya taka muhimmiyar rawa wajen gyaruwar lamuran shugabancin a kowane mataki. Rashin gyaruwar shugabanci a ban kasa, komawa karkashin kasa kan zama mafi kyawon maslaha a wasu lokutan.

Wargajewar mangalar shugabanci a matakin karamar hukuma, kan tilasa Ciyaman nada gammon daukar mafi tarin kalubale sama da kowa a mazaɓar. Gwamna a jiha, dole ya kalli kansa a matsayin babba juji sama da kowa cikin jihar. A matakin kasa kuwa, shugaban kasa ne zai rungumi mafi tarin korafe-korafen jama’a sama da kowa a kaf fadin Kasar.

Shugabancin masu mulki ne ke da iko na yankan shakku, wajen tursasa wasu karkatattun shugabanci zuwa ga mikewa sama da kowa. Saboda haka, gyaruwarsu kan zama wani abu mai alfanu sama da akasarin nau’ikan shugabancin da ke wanzuwa a tsakankanin al’umar Duniya.

Idan idanun shugabanci ya dode, tunaninsa kacokan ya koma ga mene ne zai yi habzi da shi daga al’uma, sai a saurari gurɓacewar lamura a Kasa bakidaya.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: Nijeriya
ShareTweetSendShare
Previous Post

Me Ya Sa Shawarar Tsarin Shugabancin Duniya Ta Samu Goyon Baya Daga Sassan Kasa Da Kasa

Next Post

Fadar Shugaban Ƙasa Ta Sanar Da Dalilin Korar Hadimin Shettima Kan Bunƙasa Tattalin Arziƙi

Related

Sojojin Nijeriya Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 139, Sun Cafke 132 A Cikin Sati 2 —Hedikwatar Tsaro
Manyan Labarai

Sojoji Sun Ceto Mutane 30 Da Aka Yi Garkuwa Da Su, Sun Kashe ‘Yan Ta’adda Da Dama

7 hours ago
Rashin Tsaro Ya Sa Ƴan Gudun Hijira Mamaye Makarantun Benuwe Da Neja Da Katsina
Manyan Labarai

Dawowa Hutu Ya Tayar Da Hankalin Iyaye Saboda Ƙarin Kuɗin Makaranta

9 hours ago
Likitoci
Manyan Labarai

NARD Ta Janye Yajin Aikin Gargaɗi Da Ta Fara

10 hours ago
Rashin Tsaro Ya Sa Ƴan Gudun Hijira Mamaye Makarantun Benuwe Da Neja Da Katsina
Manyan Labarai

Rushewar Masa’antu Ya Jefa Al’umma Da Dama Cikin Ƙangin Talauci A Arewacin Nijeriya

14 hours ago
Dangote Ya Sake Zama Wanda Ya Fi Kowa Kudi A Afrika Karo Na 12
Manyan Labarai

DAPPMAN Ta Soki Matatar Dangote Kan Rage Farashin Man Fetur

22 hours ago
An Tsinci Gawar Ɗalibar Jami’ar Taraba A Ɗakin Saurayinta
Manyan Labarai

An Tsinci Gawar Ɗalibar Jami’ar Taraba A Ɗakin Saurayinta

1 day ago
Next Post
Fadar Shugaban Ƙasa Ta Sanar Da Dalilin Korar Hadimin Shettima Kan Bunƙasa Tattalin Arziƙi

Fadar Shugaban Ƙasa Ta Sanar Da Dalilin Korar Hadimin Shettima Kan Bunƙasa Tattalin Arziƙi

LABARAI MASU NASABA

Duba Ga Kwaɗayi Da Son Duniya A Tsakanin Matan Wannan Zamanin

Duba Ga Kwaɗayi Da Son Duniya A Tsakanin Matan Wannan Zamanin

September 14, 2025
Jagororin Kamfanonin Ketare Sun Nuna Gamsuwa Dangane Da Zuba Jari A Kasar Sin

Jagororin Kamfanonin Ketare Sun Nuna Gamsuwa Dangane Da Zuba Jari A Kasar Sin

September 14, 2025
Bayan Fara Kamen Mabarata, An Samu Dalar Amurka, Wuƙa A Kwara

Bayan Fara Kamen Mabarata, An Samu Dalar Amurka, Wuƙa A Kwara

September 14, 2025
Ina Fatan Watsi Da Harkar Fim Nan Gaba —Umar Hassan

Ina Fatan Watsi Da Harkar Fim Nan Gaba —Umar Hassan

September 14, 2025
An Kammala Baje Kolin Hada-Hadar Cinikayyar Hidimomi Na Sin Na Shekarar 2025

An Kammala Baje Kolin Hada-Hadar Cinikayyar Hidimomi Na Sin Na Shekarar 2025

September 14, 2025
Fadar Shugaban Ƙasa Ta Sanar Da Dalilin Korar Hadimin Shettima Kan Bunƙasa Tattalin Arziƙi

Fadar Shugaban Ƙasa Ta Sanar Da Dalilin Korar Hadimin Shettima Kan Bunƙasa Tattalin Arziƙi

September 14, 2025
Shugabanci A Nijeriya: A Ina Ne Gizo Ke Saƙar?

Shugabanci A Nijeriya: A Ina Ne Gizo Ke Saƙar?

September 14, 2025
Me Ya Sa Shawarar Tsarin Shugabancin Duniya Ta Samu Goyon Baya Daga Sassan Kasa Da Kasa

Me Ya Sa Shawarar Tsarin Shugabancin Duniya Ta Samu Goyon Baya Daga Sassan Kasa Da Kasa

September 14, 2025
Sama Da Fam Biliyan Uku Aka Kashe A Firimiyar Ingila Wajen Sayen Ƴan Wasa

Sama Da Fam Biliyan Uku Aka Kashe A Firimiyar Ingila Wajen Sayen Ƴan Wasa

September 14, 2025
Me Ya Sa Bayern Liverkusen Ta Kori Erik Ten Hag Bayan Wasanni Biyu?

Me Ya Sa Bayern Liverkusen Ta Kori Erik Ten Hag Bayan Wasanni Biyu?

September 14, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.